1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya na rufe iyakokinsu

Binta Aliyu Zurmi
January 25, 2021

Kasashen duniya da dama na daukar tsauraran matakai a kan iyakokinsu a saboda kara bazuwar cutar corona.

https://p.dw.com/p/3oMVf
USA Washington | Joe Biden im Oval Office
Hoto: Tom Brenner/REUTERS

Wannan na zuwa ne bayan da a karshen makon da ya gabata alumma a kasar Netherlands suka yi boren adawa da matakan kariya daga cutar lamarin da ya kai ga dauki ba dadi tsakanin su da jami'an tsaro.

Shugaban kasar Amirka Joe Biden a wannan rana ta Litinin ce zai maida dokar haramta wa wadanda ba yan kasar ba da ke fitowa  daga kasashen Birtaniya da Brazil da ma wasu da dama a nahiyar Turai shiga kasar.

Masana kiwon lafiya na ci gaba da bayyana hanya guda ta kawo karshen wannan cutar ita ce yawaitar alurar rigakafi.