Tsaurara matakan tsaro a Faransa | Labarai | DW | 12.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsaurara matakan tsaro a Faransa

Shugaban Faransa Francois Hollande ya bukaci rundunar sojin kasar da ta shiga a dama da ita wajen tsaurara matakan tsaro a kasar.

Ministan tsaron kasar Jean-Yves Le Drian ya ce shugaba Hollande ya yanke wannan shawarar ce bayan wani taron koli kan tsaro da aka gudanar a wannan Litinin din, inda aka yanke hukuncin girke jami'an tsaron kimanin dubu 10 don tsare al'ummar kasar daga duk wata barazana da ka iya tasowa.

Daga cikin irin wuraren da za a fi maida hankali a kai sun hada da makarantu na Yahuduwa kimanin 717 da ke fadin kasar da wuraren ibada da kuma sauran muhimman wurare na haduwar jama'a.

Wannan yunkuri da ake kokarin yi dai shi ne irinsa mafi girma da aka taba gani a tarihin Faransa kamar yadda hukumomin kasar suka shaida.