1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Tsaro lokacin yakin neman zabe

Mouhamadou Awal Balarabe
November 3, 2022

Bayan da Amirka da wasu kasashen yammaci suka ja hankalin Tarayar Najeriya kan yiwuwar kai harin ta'addanci musamman a Abuja, gwamnatin kasar ta yi watsi da gargadin tare da tsaurara matakan tsaro a birnin tarayya.

https://p.dw.com/p/4J0j3
An taba kai harin ta'addanci a AbujaHoto: Reuters

Sanarwar da ofisohin jakadancin Amirka da Birtaniya da Italiya suka fitar kan yiwuwar kai hare-haren ta’adanci a Abuja babban birnin Najeriya ta haifar da martani da zaman zullumi duk da matakan tsaro da ake kara dauka. Sai dai hukumin tsaro a Najeriya sun yi watsi da gargadin kai hare-hare a babban birnin tarayya Abuja da wasu manyan kasashen yammacin duniya suka yi. Hasali ma dai, rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kara tsaurara tsaro a fadin kasar daidai lokacin da Amirka ta umurci ma'aikatan jakadancinta da zamansu bai zama dole a kasar ba su fice daga Abuja bisa yiwuwar kai hare-hare.