Tsananin zafi a Turai | Duka rahotanni | DW | 08.08.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

Tsananin zafi a Turai

Tsananin zafin da wasu kasashen Turai ciki har da Jamus ke fuskanta a halin yanzu ya janyo asarar miliyoyin euro ga manoma da kuma masu sufurin jiragen ruwa. Shuke-shuke na furanni da bishiyoyi a cikin gari da wuraren shakatawa duk sun fara bushewa. Mazauna a birnin Bonn sun yi tururwa zuwa wuraren da ke da dausayi. Ahmed Salisu ya hada mana rahoto kan wannan batu.