1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsananin damuwa ga yara 'yan kabilar Yazidi

Matthias von Hein ATB/MNA
August 3, 2020

Kungiyar Amnesty a wani rahoto ta ce kananan yara 'yan kabilar Yazidi marasa rinjaye wadanda suka tsira bayan fuskantar azbatarwa a hannun IS a Iraki suna fama da matsaloli da ke bukatar taimakon gaggawa.

https://p.dw.com/p/3gMF6
Symbolbild: Jesiden auf der Flucht
Hoto: picture-alliance/Y. Akgul

Yara 'yan Yazidi da dama an kashe su a lokacin da 'yan kungiyar IS suka mamaye yankinsu a shekarar 2014 wato shekaru shidda da suka wuce. Yaran kimanin dbu biyu aka tabbatar da sun tsira sai dai kuma ba sa samun taimakon da suke bukata. Da dama daga cikin yaran sun fuskanci ukuba ta bautar da su da aka yi a matsayin bayi da fyade da kuma kokarin sauya musu tunani. Kungiyar Amnesty ta ce an bar yaran kara zube inda a yanzu kusan dukkaninsu ke bukatar taimako da kulawa ta tsawon lokaci kamar yadda ta nunar a cikin rahoton da ta wallafa gabanin cika shekaru shidda da kisan kiyashi da aka yi wa 'yan Yazidi. Farfesa Jan Ilhan Kizilhan daya daga cikin wadanda suka wallafa rahoton ya yi tsokaci yana mai cewa.

"Babu wadatattun masana kimiyyar halayya da ma'aikatan kula da walwala da jin dadin al'uma da likitoci da masu kula da lafiyar kwakwalwa wadanda za su iya lura da wadannan yara da magidanta da suka shiga halin dimuwa. A gaskiya na kwashe shekaru shidda ina wannan nazari. Shi yasa na ke horar da masu kula da lafiyar kwakwalwa bisa tsarin dokokin Jamus tun shekarar 2017 yadda akalla za a sami makoma mai kyau da kuma samun wadanda za su iya warkar da wadannan yara." 

Jan Kizilhan na cibiyar horar da masu kula da masu tabin hankali a arewacin Iraki.
Jan Kizilhan na cibiyar horar da masu kula da masu tabin hankali a arewacin Iraki.Hoto: picture-alliance/dpa/A. Martins

Kizilhan kwararren masani ne kan kula da lafiyar kwakwalwa kuma shugaban cibiyar kula da masu tabin hankali da ke kudancin Jamus. Ya tattauna da dubban mutane wadanda suka taba fadawa hannun 'yan kungiyar IS yana kuma taimakawa wajen horar da masu kula da masu tabin hankali a arewacin Iraki.

"Mun sami yanayi inda yara 'yan shekaru takwas aka yi musu fyade ba iyaka a wasu lokutan ma har tsawon shekara daya ko biyu ko fiye da haka. An lalata musu rayuwa ta kai ba sa son haduwa da manyan mutane maza ko da kuwa 'yan uwansu ne ko iyayensu maza. Ana iya ganin tasirin dimuwar da suka samu a fannoni da dama na rayuwarsu da kuma alamu da suka baiyana."

A watan Maris na 2019 magoya bayan IS da 'yan Yazidi da aka sace a tsaunin Baghouz
A watan Maris na 2019 magoya bayan IS da 'yan Yazidi da aka sace a tsaunin BaghouzHoto: Reuters/I. Abdallah

Rahoton na Amnesty ya fayyace karara daukin gaggawa da wadannan yara ke bukata. An tattauna da yara da dama maza da mata wadanda suka baiyana irin ukubar da suka sha da cin zarafi da tilasta musu daukar makamai su yi yaki a lokacin da suke tsare a hannun 'yan IS.

A bisa alkaluman da gwamnatin lraki ta Kurdawa da ke Dohuk ta fitar, yara 'yan mata 'yan kabilar Yazidi marasa rinjaye 1041 aka 'yanto daga hannun 'yan IS a watan Fabrairun 2020. Yawancinsu sun fuskanci cin zarafi ta hanyar lalata. Haka su ma yara maza sun fuskanci irin wannan cin zarafi da tilasta musu aikin soji.

Amnesty ta kuma ba da wasu shawarwari ga mahukuntan Iraki da Kurdawa da kuma gamaiyar kasashen duniya. Bayan bukatar kula da ilmin yaran da sama musu cikakkun takardu na shaidar asali, kungiyar ta kuma yi kira ga al'ummar Yazidi ta karbi yaran da 'yan mata da aka yi wa fyade.

Düzen Tekkal ta kungiyar agaji ta Hawar Help kuma 'yar jarida, ta sha kai komo a arewacin Iraki
Düzen Tekkal ta kungiyar agaji ta Hawar Help kuma 'yar jarida, ta sha kai komo a arewacin IrakiHoto: L. Chaperon

Düzen Tekkal wata jami'ar kungiyar agaji ce kuma 'yar jarida wadda ta sha kai komo a arewacin Iraki domin nema wa yaran sa'ida, ta ce duk da cewa an kubutar da su amma har yanzu ba su sami cikakken 'yanci ba.

"Muna magana ne a kan yaran da suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira wadanda ake watangaririya da su daga wannan waje zuwa wancan waje. Wadanda aka haife su cikin halin rashin tabbas da rashin kwakkyawar makoma. Idan an yi magana sai a ce an 'yanto su daga 'yan IS, to amma har yanzu muna gani ba su sami cikakken 'yanci ba ba a ba su kariya ba, suna cikin hadari.

Ta kara da cewa a matsayinsu na yara ya kamata a kare hakkinsu tare da samar musu abubuwan bukatun rayuwa kamar wutar lantarki da ruwan sha da gina musu muhalli. Hasali ma muna bukatar yanki guda na Yazidi da kare musu rayuwarsu a ko ina a duniya.