1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka tsakanin Rasha da Czech

April 19, 2021

Hukumomi a Rasha sun bai wa wasu ma'aikatan diplomasiya 20 yan asalin jamhuriyar Czech sa'oi 24 da su fice daga kasar.

https://p.dw.com/p/3sCoP
Russland | Vladimir Putin
Hoto: Alexei Druzhinin/Sputnik/AP/picture alliance

Tun da fari Czech din ta zargi ma'aikatan diplomasiyar Rasha 18 da leken asiri, kuma tuni ta koresu.

Fira-ministan kasar ta Czech Andrej Babis ya ce bayanan sirri da suka samu sun tabbatar da cewa Rashar na da hannu a mummunan harin da ya hallaka yan kasarta biyu a gabacin kasar tun a shekara ta 2014.

Sai dai Rasha ta musunta wannan zargin, inda ta ce kasar ta Czech na kokarin dadada wa Amirka da kawayenta ne kawai.