1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaiko kan taron zaman lafiya

July 22, 2014

Wakilai daga tsohuwar kungiyar tawayen Seleka sun kauracewa taron sulhu na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ke wakana a kasar Kwango

https://p.dw.com/p/1Cgd4
Zentralafrikanische Republik
Hoto: Getty Images/AFP/Pacome Pabandji

Wakilai daga tsohuwar kungiyar tawayen Seleka na kasar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun sake kauracewa wuni na biyu na tattaunawar sulhun da ke gudana a Brazzaville na kasar Kwango, domin ganin an kawo karshen zud da jinin da ke afkuwa a kasar. An dakatar da manyan zaman sulhuntawar guda biyu sakamakon rashin kasasncewar wannan kungiyar a taron da aka shirya na dakile rikicin da kuma tabbatar da cewa kowani bangare ya kwance damara.

An ci gaba da zama na uku wanda ta danganci sauyi na siyasa bisa bukatar kungiyar raya kasashen yankin tsakiyar Afirka wato ECCAS.

Wata majiyar Kwango ta fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an bai wa kungiyar Seleka daftarin kudurin da za a rattaba wa hannu a gobe Laraba, sadda za a kammala taron, kuma wannan daftari ne suke nazari. Kimanin jami'ai 170 daga kasashen yankin Tsakiyar Afirka ke halartar wannan taro a ciki har da mambobin gwamnatin Catherine Samba Panza kuma suna samun goyon bayan manyan kasashen duniya.

Mawallafiya: Piando Abdu Waba
Edita: Suleiman Babayo