Tsageru sun halaka sojojin Mali 54 | Labarai | DW | 02.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsageru sun halaka sojojin Mali 54

Tsageru sun halaka sojojin Mali 54 sakamakon hari cikin yankin arewacin kasar da ake samun kungiyoyin 'yan ta'adda masu dauke da makamai.

Ya zuwa yanzu hukumomin kasar Mali sun tabbatar da cewa adadin sojojin da suka mutu a wani harin kwanton bauna ya kai 54, kamar yadda mai magana da yawun gwamnati Yaya Sangare ya fitar cikin wata sanarwa. Tun farko wata sanarwar soja ta ce kimanin sojoji 20 sun tsira daga farmakin wanda ya faru a wannan Jumma'a da ta gabata.

Babu wanda ya dauki alhakin hari amma ana danganta harin kan kungiyoyin tsageru masu kaifin kishin addinin Islama. An kai wannan hari a yankin arewacin kasar kusa da iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Sabon hari na zuwa kasa da wata guda bayan makamancinsa ya halaka sojojin Mali kusan 40. Arewaci da tsakiyar Mali dai na cikin tsaka mai wuya na hare-haren ta'addanci sakamakon tawayen 'yan aware da ya samo asali daga shekara ta 2012.