Tsagaita zanga-zanga a Hong Kong | Labarai | DW | 05.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsagaita zanga-zanga a Hong Kong

Masu zanga-zangar neman dimokaraɗiyya a Hong Kong, sun sanar da janyewar wucin gadi daga wasu ɓangarorin da suka mamaye a kan titunan zuwa gidan gwamnati.

Dalibai sun sha alwashin ci gaba da kasancewa a kan tituna a dai-dai lokacin da wa'adin janyewa daga kan titunan ya ke shirin cika. Ƙungiyar Occupy Central, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke jagorantar zanga-zangar ta sanar da cewar za su janye daga yankin Mongkok da kuma hanyoyin da za su kai ka zuwa gidan gwamnatin ƙasar, inda suka ce za su koma su haɗa karfi a waje guda domin ci gaba da zanga-zangar tasu. Kimanin mako guda ke, nan da al'ummar Hong Kong ɗin suka haddasa tsayawar al'ammura,sakamakon zanga-zanga da zaman dirshan da suke gudanarwa domin neman tabbatar da 'yantacciyar dimokaraɗiyya. Masu zanga-zangar dai na buƙatar shugaban gwamnatin yankin ya sauka daga muƙaminsa da kuma neman ƙasar China ta sakar musu mara domin yin fitsari ta hanyar tsame hannunta daga sha'anin siyasar