Tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra′ila | Labarai | DW | 26.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila

An fara aiki da wata yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon sa'aoi 12 tsakanin gwamnatin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu, domin samun wata kafa ta ayyukan jin kai.

Jami'an kungiyar Hamas sun ce, sun amince da yarjejeniyar bisa roko da suka samu daga MDD. Rundunar sojin Isra'ila ta ce za ta mutunta yarjejeniyar saboda samun shigar da kayayyakin agaji zuwan yankin na Zirin Gaza da ya kwashe tsawon lokaci yana fuskanatar luguden wuta daga Isra'ila.

Yanzu haka Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry yana birnin Paris na kasar Faransa, domin kara tattaunawa bisa shirin tsagaita wuta mai dorewa tsakanin bangarorin na Isra'ila da Hamas.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar