1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikice

Yarjejeniyar kawo karshen rikicin Libiya

Suleiman Babayo AS
September 26, 2018

Gwamnatin Libiya ta bayyana tsagaita wuta da tsageru masu dauke da makamai bisa matakan kawo karshen rikicin da aka kwashe wata guda ana fafatawa tsakanin bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/35Y53
KämpferLibyen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. B. Khalifa

Gwamnatin Libiya da ke samun goyon bayan kasashen duniya ta bayyana shirin tsagaita wuta domin kawo karshen fada da tsageru masu dauke da makamai kimanin watan guda ke nan a kudancin birnin Tripoli fadar gwamnatin kasar, inda fiye da mutane 100 suka rasa rayukansu, sannan wasu fiye da 400 suka jikata.

Wata sanarwar ma'aikatar cikin gida ta ce wakilan bangarorin sun saka hannu kan yarjejeniyar a garin Tarhuna da ke kudu maso gabashin birnin na Tripoli. kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka tana tsunduma cikin yakin basasa tun shekara ta 2011 bayan kawo karshen gwamnatin Marigayi Shugaba Mu'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.