1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas da Isra'ila sun tsagaita wuta

Yusuf Bala Nayaya
July 21, 2018

Kungiyar Hamas ta ayyana tsagaita bude wuta ga Isra'ila a yankin Gaza kamar yadda mai magana da yawun kungiyar ya bayyana a ranar Asabar, abin da ke zuwa kwana guda bayan kisan Falasdinawa hudu da sojan Isra'ila guda.

https://p.dw.com/p/31rAf
Palästina Israel fliegt nach Schüssen auf Soldaten massive Luftangriffe in Gaza
Hoto: Getty Images/AFP/B. Taleb

Mai magana da yawun kungiyar ta Hamas Fawzi Barhoum ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa sun cimma wannan matsaya ce da wadanda ya kira masu mamaya bisa sanya bakin Masar da Majalisar Dinkin Duniya. Ita kuwa me magana da yawun sojan na Isra'ila bayyanawa ta yi cewa ba za ta yi wani jawabi ba da ya shafi siyasa, kuma a cewarta Isra'ila yanzu ba ta kai wani hari a yankin na Gaza. A nasa bangaren Jonathan Conricus da ke magana da yawun ma'aikatar tsaron Isra'ila ya ce daga ranar Juma'a sun kai farmaki 60 da ya hada da afkawa bataliyar mayakan Hamas sau uku.