Tsagaita bude wuta a Siriya | Labarai | DW | 07.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsagaita bude wuta a Siriya

Shugaban Masar ya bayyana yiwuwar tsagaita bude wuta a Siriya nan bada jimawa ba.

Shugaba Mohammed Morsi na kasar Masar ya bayyana fatan cewar nan bada dadewa ba za'a cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar Siriya, inda dubbanin jama'a suka rasa rayukansu, a rikicin kasar wanda dakarun gwamnati da kuma 'yan tawaye suka yi tsawon kimanin shekaru biyu suna gumurzu a tsakanin su. Shugaba Morsi, ya bayyana cewar, wani taron daya gudana a tsakanin kasashen Masar da Turkiyya da kuma Iran a gefen taron koli na kungiyar kasashen Musulmi a birnin alQahira na kasar Masar, ya tattauna matakan shawo kan rikicin na Siriya.

Shugaba Morsi ya shaidawa taron manema labarai na hadin gwiwa a tsakaninsa da takwarai aikinsa na Turkiyya Abdullah Gul cewar, abinda ke da muhimmanci a yanzu, shi ne kawo karshen zubar da jinin da ake yi a Siriya. Domin cimma wannan burin kuwa - a cewar shugaban na Masar, tilas ne sassan da ke cikin rikicin su cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba tare da wani lokaci ba, yarjejeniyar da kuma ya ce - da yardan Allah za a cimma nan kusa.

Dama dai taron kungiyar hada kan kasashen Musulmi na OIC ya bukaci warware rikicin na Siriya cikin ruwan sanyi kuma ta hanyar tattaunawa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu