Tsafin shugabanin Nigeria sun sace a ƙalla dalla milion dubu 384 inji Nuhu Ribaɗo | Labarai | DW | 20.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsafin shugabanin Nigeria sun sace a ƙalla dalla milion dubu 384 inji Nuhu Ribaɗo

Shugaban hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin Nigeria zagwan ƙasa, Malam Nuhu Ribaɗo, ya zargi tsafin shugabanin ƙasar,da sace kuɗaɗen da yawan su, ya tashi a ƙalla, dalla milion dubu 385, daga samun yancin kan NIgeria, a shekara ta 1960, zuwa yanzu.

Ya ce wannan kuɗaɗe, na fitar hankali,sun lunka har sau 6, yawan kuɗin da Amurika ta baiwa ƙasashen turai, bayan yaƙin dunia na 2, domin su falfaɗo daga yaƙin da yayi masu kaca-kaca.

Nuhu Ribado ,ya ce hukumar EFCC, ta yi nasara ƙwato kudaden da yawan su, ya kai naira milion bubu 68 daga wasu tsafin magabata 2 na Nigeria, ya kuma bayyana aniyar ci gaba da wannan yaƙi, kamin zaɓen da za ayi, a ƙasar a watan Aprul na shekara mai zuwa.