Tsadar rayuwa a Zimbabwe | Labarai | DW | 17.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsadar rayuwa a Zimbabwe

Hukumomin Zimbabwe ,sun bayyana ci gaba da sa ido ga matakinda su ka dauka na yaki da hauhawan parashen kayyayakin massarufi.

Shugaban ƙasa Robert Mugabe da kansa ya jagoranvci taron jam´iyar s ata ZANU PF inda su ka tantana, a game da sakamakon da matakin ya haifar.

A cewar kakakin komitin kulla da sa idon, an cimma gagaramar nasara, ta ƙayyade parashen kaya.

Tun ranar 26 ga watan yuni da ya wuce, gwamnati ta umurci yan kasuwa su karya parashen kaya, da kashi 50 bisa 100.

Ya zuwa yanzu, yan kasuwa dubu 3 na cikin kurkuru, a sakamakon taurin kann da su ka nuna, ta fannin watsi da umurnin gwamnatin.