1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Za a kai bakin haure a garuruwan adawa

Gazali Abdou Tasawa
April 13, 2019

Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya yi barazanar aikawa da tarin bakin hauren da aka kama kan iyakar kasar ake tsare da su, zuwa wasu manyan birane wadanda jam'iyyyar adawa ta Democrates ke da karfi a cikinsu. 

https://p.dw.com/p/3GiNc
USA Donald Trump  in San Antonio
Hoto: Reuters/C. Barria

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tweeter, Shugaba Trump ya ce ta la'akari da yadda 'yan jam'iyyar Democrates ke nuna adawa ga bukatarsa ta daukar sabbin dokoki na tsaurara matakan hana kwararar bakin haure zuwa kasar, ya soma nazarin yiwuwar aikawa da tarin bakin hauren da ake tsare da su zuwa biranen San Francisco ko Shicago wadanda suke bayar da mafaka da ma kariya ga tarin bakin haure da ke da zama a cikinsu, da kuma kim ba da hadin kai ga jami'an yaki da bakin haure a kasar. 

A sakon nasa Shugaba Trump ya yi shguban cewa ya yi imanin wannan mataki nasa zai faranta wa jam'iyar adawar ta Democrate da rai matuka. Sai dai magadan garuruwa da dama daga cikin wadanda shugaba Trump ya yi barazanar aika masu da bakin hauren, sun mayar da martanin cewa a shirye suke su karbi duk wasu bakin hauren da zai aiko a cikin garuruwan nasu.