1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Trump yace an kusa cimma yarjejeniya tsakanisa da Iran

May 23, 2026

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Iran na kara kusantar cimma yarjejeniya domin kawo karshen yakin da aka shafe kusan watanni uku ana yi.

https://p.dw.com/p/5EEho
Shugaban Amurka DonalD Trump
Shugaban Amurka DonalD TrumpHoto: Saul Loeb/AFP

A wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta CBS, Trump ya ce yarjejeniyar za ta hana Iran mallakar makamin nukiliya, tare da tabbatar da cewa an dauki matakin da ya dace kan sinadarin uranium da Iran ta tace.

Trump ya ce ba zai sanya hannu kan wata yarjejeniya ba sai idan Amurka ta samu duk abin da take bukata.

Iran da Amurka tare da Pakistan da ke shiga tsakani sun ce an samu cigaba a tattaunawar da a ke yi domin kawo karshen rikicin.

A wata hira daban da ya yi da kafar yada labarai ta Axios, Trump ya ce zai tattauna da masu ba shi shawara kan sabon daftarin yarjejeniyar Iran, wanda zai tabbatar da yanke hukuncin ci gaba da yakin ko akasin haka.

Trump ya kuma gargadi Iran da cewa idan ba a cimma kyakkyawar yarjejeniya ba, zai dauki tsauraran matakai.