Trump ya yi wa Falasdinawa barazana | Labarai | DW | 03.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya yi wa Falasdinawa barazana

Kasar Amirka ta yi barazanar janye agajin miliyoyin dalolin da take bai wa Falasdinawa da adadin ya kai dala miliyan 300 a shekara.

Shugaban Amirka Donald Trump ya yi barazanar janye agajin da Amirkar ke bai wa Falasdinawa da adadinsa ya kai dala miliyan 300 a shekara. Shugaban na Amirka wanda ya sanar da hakan ta shafinsa na Twitter, ya kuma amince cewar shirin samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya dai na cikin wani hali. Mr. Trump ya ce kudaden Amirkawa na tafiya ga banza ba tare da mutunta kasar ba.

Sai dai fa wasu na ganin wannan barazana ta Mr Donald Trump, tamkar siyasa ce, ganin yadda ya yi tutiyar samar zaman lafiya a gabas ta tsakiya, da kuma ya gagari shugabanni tun cikin shekarun 1960.