1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar wakilan Amirka ta tsige Trump

Abdourahamane Hassane
January 14, 2021

Shugaban Amirka mai barin gado Donald Trump ya sake nisanta kansa daga kutsen da wasu magoya bayansa suka yi a majalisar kasar.

https://p.dw.com/p/3nuAY
US-Präsident Donald Trump
Hoto: Donald J. Trump via Twitter/REUTERS

Wannan dai al'amari na tsige shugaban Amirkan da majalisar ta yi, ya dau hankal kasashen duniya, ko da shi ke ma hukunci ba shi da tasiri kai tsaye sai idan har majalisar dokoki ita ma ta kada kuri'a tsige shugaban. To amma da yake magana jim kadan bayan majalisar wakilan kasar ta sanar da tsige shi daga madafun iko, Trump ya ce babu wani wanda ya fi karfin doka a Amirka, yana mai ikirarin cewa masoyinsa na zahiri ba zai aikata irin wannan ba. Ya sha alwashin sai an hukunta duk mutanen da suka yi kutsen.