1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya sa dokar ta baci kan Mexiko

Abdul-raheem Hassan
February 15, 2019

Shugaba Donald Trump na Amirkan ya ce matakin na da nasaba da tabarbarewar tsaro a kan iyakar Mexiko da Amirka, kuma a shirye ya ke ya fuskanci kalubalen shari'a da na 'yan adawa kan matakin.

https://p.dw.com/p/3DUD3
USA Washington - Präsident Trump und Mike Pence
Hoto: picture-alliance/Newscom/O. Douliery

Trump ya ce matsalar tsaro da ke faruwa a kan iyakar Mexico da Amirkan ta tsananta kuma za ta iya shafar tsaron kasa, a dangane da haka wajibi a samar da kudin gina katangar a tsakanin kan iyakokin kasashen biyu, ko da kuwa kudurin zai fuskanci tirjiya a majalisa da kuma kotu ya na mai cewa: "Na sa hannu kan dokar, kuma na sani mataki na gaba shi ne a kai batun kotu, kuma za mu iya gaza yin nasara a matakin farko. Amma daga karshe za mu karkare a kotun koli, inda muke fatan samun nasarar."