Trump ya janye tura sojoji kan zanga zanga | Labarai | DW | 03.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya janye tura sojoji kan zanga zanga

Trump ba zai tura sojoji don kwantar da tarzoma ba yayin da masu zanga zangar adawa da 'yan sanda kan mutuwar George Floyd suka bujire ma dokar hana fita a fadin Amirka

Shugaban Amirka Donald Trump ya sassauta barazanar tura sojoji domin tarwatsa masu zanga zanga a jihohin kasar inda fadar gwamnati, White House ta ce gwamnatocin jihohi za su iya shawo kan lamarin domin maido da doka da oda.

Mai baiwa shugaba Trump shawara kan harkokin tsaro Robert O'Brien ya shaidawa 'yan jaridu cewa gwamnati za ta hada kai da gwamnonin jihohi da magadan garuruwa domin tabbatar da tsaro a yankunansu

Sauyin matsayin na Trump na zuwa ne yayin da zanga zangar ta ci gaba babu kakkautawa a Washington da sauran manyan birane domin nuna bacin rai game da wariya da cin zarafi da ake nunawa tsirarun kabilu a Amirka.

Zanga zanga ta barke fadin Amirka sakamakon mutuwar George Floyd wani bakar fata wanda ya rasa ransa bayan da wani dan sanda farar fata a Minneapolis ya danne shi a kasa ya kuma sa gwiwarsa ya shake masa wuya.