Trump ya gabatar da tsarin tsaron Amirka | Labarai | DW | 19.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya gabatar da tsarin tsaron Amirka

Kundin tsarin tsaron da shugaban Amirka ya gabatar, ya nuna bukatun karafafa matakan tsaro da tattalin arzikin Amirka da zai zarta na sauran kasashe tare da fifita muradun kasar a idanun duniya.

Bayan shafe watanni 11 yana tsarawa shugaban kasar Amirka Donald Trump, ya gabatar da kundin tsarin tsaron kasa karkashin mulkinsa. Shugaban ya tsara wannan kundi ne bisa alkawuransa na farko, da zimmar fifita bukatun Amirka a duniya.

Shugaban Donald Trump ya ce "A karon farko tsarin Amirka ta yi la'akari cewar karfin tattalin arziki, shi ne tsaron kasa. Bunkasar tattalin arziki da walwala a cikin gida shi ke da muhimmanci ga tasirin Amirka dama karfin fada a jinta a tsakanin kasashen duniya. "