1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Trump ya ce ba shi da masaniyar farmakin Isra'ila a Qatar

September 10, 2025

A daidai lokacin da kasashen duniya ke ci gaba da martani kan harin da Isra'ila ta kai birnin Doha na Qatar, Shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada cewa ba shi da hannu ko kuma masaniya kan kai harin.

https://p.dw.com/p/50G0W
Shugaban Amurka Donald Trump a yayin tattaunawa da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani a birnin Doha
Shugaban Amurka Donald Trump a yayin tattaunawa da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani a birnin DohaHoto: Brendan Smialowski/AFP

Trump ya ce ba a sanar da shi shirye-shiryen kai farmakin ba, ya kara da cewa Qatar ta taka rawar gani wajen sulhunta kungiyar Hamas da Isra'ila wanda kuma ya kai ga musayar fursunonin yaki da dama tsakanin bangarorin biyu.

Karin bayani:Ba a san ba ko harin ya rutsa da 'yan Hamas

Shugaba Trump ya sanar da manema labarai cewa bayan rawar da Qatar ke takawa a matsayin mai shiga tsakani akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin Amurka da Doha wanda ko a baya bayan nan kasar ta Qatar ta karrama shugaban na Amurka tare da bashi kyautar jirgin sama na alfarma.

Karin bayani:Isra'ila ta dau alhakin kai wa jagororin Hamas a birnin Doha na Katar

A daidai lokacin da Qatar ke shirye-shiryen ramuwar gayya, Shugaba Trump ya umarci Sakataren Harkokin Wajen Kasar Marco Rubio da ya jagoranci tattaunawar samar da zaman lafiya da hukumomin Doha. Trump ya kara da cewa ya tattauna da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ta wayar tarho tare da bashi tabbacin kare kasar Qatar daga duk wata barazana a nan gaba.

.