Trump ya amince ya gana da Kim Jong Un | Labarai | DW | 09.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya amince ya gana da Kim Jong Un

Shugaban Donald Trump na Amirka ya amince ya gana a nan gaba da Shugaba Kim Jong Un na kasar Koriya ta Arewa, wanda a baya suka sha jifan juna da muyagun kalamai.

Babban jami'in gwamnatin kasar Koriya ta Kudu ne dai Chung Eui-Yong ya sanar da labarin, bayan wata ganawarsa da Shugaban na Amirka Donald Trump. Kuma a cewar mai magana da yawun ministan kula da hadin kan kasashen koriya biyu, wannan matsayi da aka cimma ba wai kokarin ne na bangariri da dama.

"Sakamakon ayyukan da muka gani yanzu ba kawai kokarin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu ne ba, taimako daga  Amurka ya taka muhimmiyar rawa.  Kuma muna tsammanin saboda gwamnatin Koriya ta taka muhimmiyar rawa wajen karfafawa ta hanyar shirin nan na Berlin, don matsa lamba da kuma fara tattaunawa."

Wani kusa a gwamnatin ta Amirka ya tabbatar da wannan batu, inda ya ce shugaban na Amirka bai samu wata wasika daga shugaban Koriya ta Arewa ba, amma an sanar masa da gayyata ta baki. Sai dai ya zuwa yanzu ba a sanar da wuri da kuma ranar da za a yi wannan haduwa ba.