Trump na shan suka kan birnin Kudus | BATUTUWA | DW | 07.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Trump na shan suka kan birnin Kudus

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da la'antar shugaban Amirka bayan daukar matakin tabbatar da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.

Gwamnatin kasar Turkiyya karkashin Shugaba Racep Tayyip Erdogan na daga cikin wadanda suka yi kakkausan suka a kan wannan kuduri, inda ya ce amincewar Amirkar ta sauya birnin Kudus a matsayin fadar mulkin Isra'ila ya saba da tsarin Majalisar Dinkin Duniya na tun shekarun 1980.

Türkei Erdogan zieht Soldaten aus Norwegen ab (Imago/Depo Photos)

Shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan

"Babu wata kasa a duniya in banda Amirka da Isra'ila da ta dauki matakin saba abin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi shekaru 37 yanzu. Su ne dai kasashe biyun da suka bijirewa hakan. Da wuya a iya fahimtar abin da shugaba Donald Trump yake nufi, da wannan abin da ya sake kawowa. Kuma mataki kamar haka, tunzura yankin ne ya shiga sabon rikici. Wai me kake ne Mr. Trump? Shugabanni na kafuwa ne saboda ci gaba amma ba haddasa husuma ba."

Shi ma dai shugaba Joko Widodo na kasar Indonisiya, kasar da ta fi yawan al'umar musulmi a duniya, ya yi Allah wadai da matakin Amirka na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.

"Indunisiya ta yi tir da kakkausar lafazi da matakin gaban kai da Amirka ta dauka na sauya hedikwatar Isara'ila. Hakan ya ci karo da abin da kwamitin sulhun MDD ya tsara, wanda ita Amirka tana daga daga cikin masu kujerar din-din-din a ciki. Lallai wannan mataki ne da zai shafi zaman lafiyar al'umar duniya. Da ni da sauran ‚yan kasar Indonesiya, muna bayan al'umar Falasdinu a yakin neman hakki da kuma ‘yanci da suke kai."

Gazastreifen Protest gegen Donald Trump, US-Präsident - Anerkennung Jerusalem als Hauptstadt (picture-alliance/Anadolu Agency/M. Hassona)

Falasdinawa na ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa da matakin na Trump

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Koriya ta Kudu ta yi tsokaci kan wannan batu, inda ta ce yin haka zai haifar da illoli ko da yake ba za iya sanin ko akwai tasiri ba kawo yanzu kamar yadda kakakin ma'aikatar Noh Kyu-Duk ya ce:

"Dangane da batun Isra'ila da Falasdinawa, gwamnatinmu ta dade da goyon bayan samar da kasashe biyu masu cikakken ‘yanci ta hanyar tattaunawa. Mun fahimci cewa, matsayin Isra'ila na karshe yana da sarkakiyar gaske, da kuma ke bukatar a warware shi cikin ruwan sanyi ba hargitsi ba."

Tun bayan bayyana sauya birnin na Kudus a matsayin fadar mulkin Isra'aila, Falasdinawa ke zanga-zangar adawa da kudurin na Amirka. Sai dai rundunar sojin Isra'ila tana kan kara dakaru zuwa yankunan da Falasdinawan suka mamaye da zanga-zangar don tsaurara tsaro.

 

Sauti da bidiyo akan labarin