Trump na garambawul a manufofin Amirka | Labarai | DW | 01.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump na garambawul a manufofin Amirka

A jawabinsa na farko a gaban majalisar hadin gwiwar kasar, shugaban Amirka Donald Trump ya jaddada manufarsa na inganta rayuwar al'ummarsa.

Ya tabo manufofin Amirka na ketare tare da sake tabbatar da goyon bayansa ga kungiyar tsaro ta NATO.

" Manufofinmu na ketare na bukatar garambawul tare da taka rawa mai ma'ana cikin lamuran duniya. Shugabanci ne da ke da muradu na tabbatar da muhimmancin tsaro da sauran abokan huldarmu da ke fadin duniya. Muna goyon bayan NATO, dangantakar da ke da alaka da yake-yaken duniya guda biyu".

Trump ya sake nanata alkawarinsa na samar da guraben aiki da gina katanga tsakanin Amirka da Mexico da cin galaba kan mayakan IS, tare da kara kudade a sashin soji, a hannu guda kuma ya sanar da sabbin dokoki da suka shafi shige da ficen kasar.