1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Fara shari'ar Donald Trump

February 9, 2021

Majalisar dattawan Amirka ta fara shari'ar tsohon shugaban kasar Donald Trump bayan da majalisar wakilai ta tsige shi a karo na biyu.

https://p.dw.com/p/3p7qr
USA Amtsenthebungsverfahren gegen Trump
Majalisar dattijan Amirka na sauraron shari'ar tsohon shugaban kasar, Donald TrumpHoto: Senate Television/AP/dpa/picture alliance

Bangaren jam'iyyar Democrats da ya shigar da kara, yana zargin Trump ne da laifin tunzura wasu magoya bayansa 'yan ta'addar cikin gida, suka kai farmaki a majalisar dokokin Amirkan, a ranar shida ga watan jiya na Janairun da ya gabat, inda suka nemi yin juyin mulki, daidai lokacin da majalisar take tabbatar da nasarar da sabon shugaban ksar Joe Biden ya samu. Kwararan hujjoji da Democrats za su gabatar a shari'ar da ita ce irinta ta farko cikin tarihin kasar da aka taba yi wa wani shugaba a Amirkan, sun hadar da hotunan ta'asar da aka yi a majalisar da kalaman da Trump ya dade yana yi, musanman wasu ‘yan mintoci kafin ya umarci magoya bayan nasa, su dunguma zuwa ginin majalisar dokokin: "Ku fafata fada tamkar na fitar-rai, saboda idan ba ku yi kazamin gumurzu ba, kasarku za ta kubuce maku"
Su kansu 'yan gani kashe nin Trump din, da yanzu haka ake tuhumar fiye da 200 cikins, suna alakanta ta'asar da suka tafka din ne da cewa sun yi ne bisa umarninsa. Ga misali abin da Jacob Anthony Chansley wani hatsababi da ya yi kwalliya da kahonni yake cewa: "Donald Trump ya umarci kowa ya koma gida. Yanzu-yanzu, ya fitar da wani sakon minti daya ta tweeter, ya ce kowa ya tafi gida."

USA Jacob Anthony Chansley Gewaltsamer Einbruch Capitol Verschwörungstheoretiker
Jacob Anthony Chansley gawurtaccen magoyin bayan tsohon shugaban Amirka TrumpHoto: Douglas Christian/Zumapress/picture alliance

Karin Bayani:Sabon kudirin neman tsige Shugaba Donald Trump

Masu kare Donald Trump kama daga Lauyoyinsa zuwa ga yawancin 'yan jam'iyyarsa ta Republican, suna ganin cewa tsohon shugaban bai yi wani laifi ba saboda sashe na daya na kundin tsarin mulki ya ba shi 'yancin fadin albarkacin bakinsa, sannan bisa doka haramun ne majalisar dattawan ta yi wa tsohon shugaba shari'a, duk da yake Democrats suna ba da misali da wani tsohon sakataren tsaro da ya taba fuskantar tuhuma a shekarar 1876.

Karin Bayani: Biden ya bayyana manufofinsa na ketare

Dangane da sigar shari'ar kuwa, an shirya cewa a wannan Talatar za a mayar da hankali ne wajen tafka dogon Turanci akan ko kundin tsarin mulki ya yarda da aiwatar da irin wannan shari'a ko kuma a'a? Masanin irin wannan dambarwa, Farfesa Laurence Tribe na jami'ar Havard ya ce: "Ina jin cewa za mu yi galaba dangane da jayayya kan abin da tsarin mulki ya tanada, a saboda tuni muna da kuri'u 55. Wannan rinjayen ake bukata."

USA, Washington I Trump Impeachment
'Yan majalisar wakilan Amirka ne dai suka mika kundin tsige Trump ga majalisar dattijanHoto: Melina Mara/The Washington Post/AP/picture alliance

Bayan wannan takin ne kuma, sai a bai wa kowane bangare sa'o'i 16 cikin wasu 'yan kwanaki, ya gabatar da hujjojinsa gaban majalisar dattawan da Amirkawa baki daya, daga bisani kuma 'yan majalisar su 100, su kada kuri'a walau a samu Trump da laifi ko a wanke shi. Sai dai ga alama bisa yadda ake adawar siyasa sosai, dakyar ne idan za a iya samun 'yan majalisa 67 da za su amince su kama Trump da laifi, musanman ganin cewa da ma a yanzu haka ana kunnen doki ne ma'ana  kowace jam'iya tana da sanatoci 50. Kodayake Trump ya ki amsa goron gaiyatar da aka yi masa dan ya ba da shaida ko kare kansa, amma majiyoyi da dama sun ce yana sa idanu sosai musanman dan ya ga 'yan jam'iyarsa a majalisar da za su juya masa baya domin nan gaba ya yi ramuwar gayya.