1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump na barazana ga yarjejeniyar nukiliyar Iran

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 25, 2018

Kasashen Birtaniya da Jamus da kuma Faransa na son shawo kan shugaban Amirka Donald Trump dangane da batun yarjejeniyar makamshin nukiliyar Iran da aka cimma a shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/2wg6S
USA PK US-Präsident Trump und französicher Präsident Macron in Washington
Shugaban Amirka Trump da takwaransa na Faransa MacronHoto: Reuters/K. Lamarque

Trump dai ya bayyana yarjejeniyar da kasashen Amirkan da Birtaniya da China da Faransa da Rasha da kuma Jamus suka cimma dangane da batun makamashin nukiliyar Iran din, da yarjejeniya mafi muni da aka taba cimma a duniya, baya ga barazanar janye kasarsa daga yarjejniyar da ya yi ta hanyar kakakabawa Iraan din sabbin takunkumi a watan Mayu mai zuwa. Tuni dai shugaban kasar ta Iran Hassan Rohani ya sanya kafa ya yi fatali da batun yin matsin lamba daga kasashen Amirka da Faransa na sake zama kan tebur domin tattauna sabuwar yarjejeniyar kasa da kasa kan makamashin nukiliyar kasarsa. Trump dai ya bukaci kasashen Turai da su sanya tsauraran matakai ga Iran kafin cimma sabuwar yarjejeniyar, wacce ya ce ita ce za ta maye gurbin ta 2015 din da aka cimma.