Trump da Macron sun halarci ranar D-Day | Labarai | DW | 06.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump da Macron sun halarci ranar D-Day

Shugabannin kasashen Turai da Amirka sun halarci gabar ruwa a Nomandy da ke Faransa, inda Amerikawa da sojojin kawance suka sauka domin bayar da gudummawar karya lagon sojojin mamaya na Nazi a nahiyar Turai.

Bbikin da ake wa lakabi da D-Day na wannan lokaacin dai shi ne karo na 75, kuma an gudanar da shi cikin yanayi na harba bindigogi a sama da faretin girmamawa. Shugaba Donal Trump na Amirka da Emmanuel Macron na kasar Faransa sun yi tsit a wurin bikin tunawa da sojojin da suka mutu lokacin yakin duniya na biyu. Sama da mutane 60 daga kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da suka tsira bayan yakin mamaya a watan Yuni na shekara ta 1944 da har yanzu suke raye sun halarci bikin na bana.