Trump da Biden na gangamin karshe | Labarai | DW | 02.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump da Biden na gangamin karshe

'Yan takarar shugaban kasar Amirka na bayyana wa magoya bayansu manufofis da tsarinsu kan kasar a gangamin yakin neman zabe na karshe a muhimman jihohi.

Shugaba Trump ya nufi jihohi biyar kama daga North Carolina zuwa Wisconsin, yayin da Biden ya fi mai da hankali kan jihar Pennsylvania da Ohio inda ya ke da kwarin gwiwar cin zabe bayan Trump ya fadi a zaben da ya gabata.

Sama da mutane miliyan 93 sun kada kuri'unsu gabannin ranar zaben, sai dai Joe Biden yana kan gaba da yawsan kuri'u a zaben jin ra'ayi da aka yi makon da ya gabata, yayin da shugaba Trump ke ikirari da magoya bayansa da ke fatan dawo da shi kan mulki karo na biyu.