Transparency International ta baiyana rahotonta na shekara 2012 | Labarai | DW | 05.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Transparency International ta baiyana rahotonta na shekara 2012

Ƙasashen duniya da dama na fuskantar mumunar barazana ta cin hanci da karɓar rashawa waɗanda suka bazu har a cikin ƙasashen ƙungiyar Tarryar Turai

A rahotonta na wannan shekara da ke shirin kammala da ta baiyana ,ƙungiyar Transparency International mai fafutukar yaƙi da cin hanci a duniya ,ta ce lamarin cin hancin da karɓar rashawa na ƙara zama babbar barazana ga ƙasashen duniya.

Kuma rahoton ya nuna cewar matsalar ta cin hanci ta shafi wasu ƙasashe na ƙungiyar Tarrayr Turai galibi masu fama da koma baya na tattalin arziki. Irin su Girka da Italiya waɗanda suka zo na 72 da kuma na 94 a jere a cikin sahun kasashe 170 da ƙungiyar ta gudanar da bincike.Ƙasashen Danmark da Finlade da Nuzilan sune ƙasheshen da suka fi rashin cin hancin a duniya

yayin da Somaliya da Koriya ta Kudu da Afganistan wanda ke a ƙarshe suka fi kowa cin hancin.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Mohammed Nasir Awal