Touadéra na kan gaba a Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 04.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Touadéra na kan gaba a Afirka ta Tsakiya

Hukumar zaben Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta nunar da cewa tsohon Firaminista Faustin Arcange Touadéra na kan gaba a zaben shugaban kasa.

Tsohon Firaministan Jamhuriyar Afirka Tsakiya kana dan takara mai zaman kansa Faustin Archange Touadéra ya yi wa sauran abokan karawarsa zarra idan aka yi la'akari da kashi daya bisa hudu na kuri'un da aka tantance. Hukumar zaben kasar ta nunar da cewar wanda ake sa ran cewar zai taka rawar gani wato Anicet Georges Dologuélé ne ke biya masa baya da yawan kuri'u

'Yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya miliyan biyu ne suka kada kuri'u a ranar Laraba da ta gabata, bayan da aka dage zabe da tsawon kwanaki uku sakamakon jinkirin da aka samu wajen raba kayan zabe da kuma horos da jami'an na zabe.

'Yan takara sama da 30 suka shiga aka dama da su a zaben na shugaban kasa, wanda ake jiran cikakken sakamakonsa. A ranar 31 ga wannan wata na Janairu ake sa ran za a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.