1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tottenham ta kai wasan karshe na zakarun Turai

Gazali Abdou Tasawa
May 9, 2019

Kungiyar Tottenham ta Ingila ta yi nasarar kaiwa wasan karshe na cin kofin zakarun Turai bayan da ta doke Ajax a gida da ci uku da biyu a wasan da suka buga a Amsterdam a ranar Laraba.

https://p.dw.com/p/3ID2u
UEFA Champions League | Ajax Amsterdam vs. Tottenham Hotspur
Hoto: Reuters/Action Images/M. Childs

A gasar cin kofin zakarun Turai, gawo ya sake juyewa da mujiya a jiya Laraba inda kungiyar Tottenham ta doke Ajax da ci uku da biyu a karawar da suka yi a filin wasa na Amsterdam Arena. Kungiyar Ajax wacce ke da ajiyar kwallo daya da ta ci tun a lokacin da ta kai bakunci a Tottenham a makon da ya gabata, ita ce ta soma zura kwallaye biyu tun kafin a je hutun rabin lokaci. 

Sai dai baya an dawo wasa ya canza inda dan wasan gaba na kungiyar ta Tottenham Lucas Mura dan asalin kasar Brazil kana tsohon dan wasan kungiyar PSG ta kasar Faransa ya yi nasarar zura kwallaye uku a jere a minti na 55 da na 56 da kuma a minti na karshe na karin lokaci. 

A yanzu dai Tottenham ta yi nasara kaiwa wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai inda za ta kara da Liverpool a filin wasan na Wanda Metropolitano na birnin Madrid a kasar Spain a ranar daya ga watan Yunin gobe. 

Wannan shi ne karo na farko a shekaru biyar na baya bayan nan da ake buga wasan karshe na cin kofin zakarun Turai ba tare da wata kungiyar La Ligar kasar Spain ba, ko kuma ba tare da Messi ke Ronaldo ba.