1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Togo: 'Yan adawa na matsin lamba ga gwamnati

Salissou Boukari
September 12, 2017

'Yan adawa a Togo sun tilasta yin zaman majalisar dokoki a ranar Talata (12.09.2017) biyo bayan jerin zanga-zangar da suke ci gaba da gudanarwa a kasar na neman kawo sauye-saye a tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/2jpRk
Togo Protest #Faure Must Go
Zanga-zangar 'yan adawa a kasar TogoHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Da alama dai tsugune ba ta kare ba a kasar Togo, ganin yadda aka yi zaman majalisar ba tare da gabatar da kudurin da 'yan adawar kasar ke nema da akawo sauye-sauye a kan su ba na kundin tsarin mulkin kasar na shekar ta 1999 ba. Inda 'yan adawar ke bukatar rage wa'adin shugabanci. Batun da ya dauki hankalin zaman majalisar dai shi ne kasafin kudin kasar na badi. Wannan ya sa Eric Dupuy mai magana da yawun babbar jam'iyar adawar kasar ta ANC, ya zargi gwamnati da yi musu kafar ungulu. A wata hira da tayi da DW ta Skype, krisellan da ke bibiyar lamuran siyasar Afirka ta yamma, naganin akwai bukatar cimma matsaya a tsakanin manyan jam'iyun kasar.

Zaman majasar dai ya gudana cikin tsauraran matakan tsaro. Wannan kuwa baya rasa nasaba da ci gaba da gudanar da zanga-zanagar da 'yan adawar ke yi gabanin zaman majalisar. yi karin haske. Siyasar kasar ta Togo dai na cikin rudani tun bayan da 'yan adawan kasar suka ayyana zanga-zanagar a sassa daban-daban na kasar, inda ko a makon da ya gabata dubban masu zanga-zangar sun cika titunan birnin Lome inda suke nuna bukatunsu na kawo karshen shugabancin iyalan Faure Gnassingbe da ke mulkan kasar tsawon shekaru 50.

An dai yi ta sauya kundin tsarin mulkin kasar ta Togo ba sau daya ba, inda ko a shekara ta 2002 ma an yi kwaskwarimar rage wa'adin shugabanci.  Amma a yanzu 'yan majalisa na cewa sauyin na bukatar lokaci dan yin nazari. A yanzu dai abin jira agani shi ne ko jan kafa da majalisar ke yi, ka iya bai wa shugaban kariya na neman tsayawa takara ko a a, inda majalisar ke sa ran sake zama kan wadannan kudirori a tsakiyar makon gobe.