1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faure Gnassingbe ya sake lashe zaben shugaban kasa

Ramatu Garba Baba
March 3, 2020

Kotu a kasar Togo ta tabbatar da nasarar Shugaban kasa mai ci Faure Gnassingbe a babban zaben shugaban kasar da zai ba shi wa'adin mulki na shekaru 5 a karo na hudu.

https://p.dw.com/p/3Yoms
Togo Präsident Faure Gnassingbe
Hoto: Imago/Xinhua

Shugaba mai ci na kasar Togo Faure Gnassingbe ya lashe babban zaben shugaban kasar da aka gudanar a makon jiya da kashi sabain da daya cikin dari. Gnassingbe zai ci gaba da jan ragamar mulkin kasar da ya soma shekaru goma sha biyar da suka bayan mahaifinsa.

Sanarwar sakamakon zaben da kotun ta yi, ta ce ya kawo karshen duk wani jan-in-ja da ya dabaibaye zaben na watan Febrairu. Kawo yanzu dai babu martani daga bangaren madugun adawa Gabriel Messan Agbeyome Kodjo da ya ce, jam'iyyarsa ce ta yi nasara da kashi sittin cikin dari na kuri'un da aka kada.

Shugaba Gnassingbe na da shekaru biyar a sabon wa'adin mulki. Tun dai daga shekara 2017 ne dai iyalan Gnassingbe suka soma fuskantar matsi daga bangaren adawa daga 'yan kasar da suka bukaci kawo karshen mulki da iyalan Gnassingbe suka kwashe shekaru 50 suna yi.