Tirka-tirkar siyasa a Maldives | Labarai | DW | 10.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tirka-tirkar siyasa a Maldives

A karo na uku cikin watanni biyu al'ummar kasar Maldives sun sake kada kuri'a a zaben shugaban kasa ba tare da samun wanda ya lashe zaben ba.

Kotun koli a kasar Maldives ta bada umurnin dakatar da fara kada kuri'u a zaben shugaban kasar zagaye na biyu, da aka shirya gudanarwa a yau Lahadi, tare da sanya ranar 16 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki a matsayin sabuwar ranar da za a gudanr da zaben na fid da gwani.

Zababben shugaban kasar bisa tafarkin dimokoradiyya na farko a Maldives din, da aka tilastawa sauka daga kan karagar mulki a shekarar da ta gabata Mohamed Nasheed, ya lashe kaso 47 daga cikin kuri'un da 'yan kasar suka kada a jiya Asabar, yayin da Yaamin Abdul Gayoom, dan uwan tsohon shugaban kasar na kama karya daya shafe shekaru 30 a kan karagar mulki wato Maumoon Abdul Gayoom, ya samu kaso 30 cikin 100 na kuri'un da aka kada, wanda hakan ya sanya tilas sai an gudanar da zagaye na biyu.

Dokar zaben kasar ta nunar da cewa dole ne sai dan takara ya lashe kaso 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada kafin a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Uamaru Aliyu