Tirka-tirkar siyasa a Bangladesh | Labarai | DW | 06.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tirka-tirkar siyasa a Bangladesh

Gwamnati a Bangladesh ta haramtawa jam'iyyar masu kaifin kishin addini shiga zabukan 'yan majalisun dokokin kasar a karshen mako.

Sakamakon farko na zabukan 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a karshen mako a kasar Bangladesh na nuni da cewa jam'iyya mai mulki ta "Awami League" ce ta lashe zaben. A kalla mutane 18 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sanadiyyar rikicin zabe a sassa daban-daban na kasar.

Rikicin dai ya balle ne bayan da masu fashin baki suka yi zargin kai hari tare da sace akwatunan zabe, wanda hakan ya tilasta dage zabuka a rumfunan zabe 200 dake sassa daban-daban na kasar. Dama dai gwamnatin kasar ta Bangladesh ta haramtawa jam'iyyar "Jamaat-e-Islami" ta masu tsattsauran ra'ayi shiga zabukan 'yan majalisun da aka gudanar, wanda kuma masu fashin baki ke ganin cewa zai sake haifar da tashin hankali a kasar.

Gabanin zabukan dai jam'iyyun adawa sun gudanar da jerin zanga-zanga daban-daban dake neman Firaministar kasar Sheikh Hasina ta sauka daga kan karagar mulki tare da nada wani na wucin gadi da zai duba yadda zabukan za su gudana, sai dai Firaminista Hasina ta yi watsi da wannan bukata ta su, inda aka haramta musu wasu ba'arin zanga-zangar da suka shirya gudanarwa. A na dai sa ran za a sanar da sakamako na karshe da zai bayyana wanda ya lashe zaben baki daya nan ba da jimawa ba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal