1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tillerson ya ziyarci Iraki

October 23, 2017

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson, ya kai wata ziyarar ba-zata birnin Bagadazan kasar Iraki a wannan Litinin domin ganawa ta biyu da Firaminista Haider al-Abadi.

https://p.dw.com/p/2mNHJ
USA Rex Tillerson in Malaysia
Hoto: Getty Images/AFP/M. Vatsyayana

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson, ya kai wata ziyarar ba-zata birnin Bagadazan kasar Iraki a wannanLitinin domin ganawa ta biyu da Firaminista Haider al-Abadi. Kazalika lokacin ziyarar, bayanai na nunin cewa Mr. Tillerson zai tattauna da shugaban kasar Iraki Fuad Masum wanda dan bangaren Kurdawa ne inda zai tabbatar masa da goyon bayan Amirka ga dunkulalliyar kasar Iraki ta yanzu.

Cikin watan jiya ne dai aka gudanar da zaben raba-gardama a arewacin kasar ta Iaki, zaben da kasar Amirka ke goyon bayansa. Wannan ziyarar, ta zo ne kwanaki biyu da sakataren harkokin wajen na Amirka Rex Tillerson ya yi kiran mayakan tawayen Iraki da su gaggauta barin kasar, abin ma da ya haifar da martani daga majalisar mukarraban firaminista al-Abadi.