Theresa May na fuskantar matsin lamba | Labarai | DW | 12.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Theresa May na fuskantar matsin lamba

'Yan majalisar dokoki a Birtaniya na shirin kada kuri'ar yanka kauna ga firaminista Therasa May

Kuri'ar yanka kaunar wacce wasu 'yan majalisar ne, na jami'yyar shugabar gwamnatin suka gabatar da ita domin tsige firaminitan, za a gudanar da ita ne zuwa da yamma. Shugabar gwamnatin ta Birtaniya Therasa May za ta iya rasa mukaminta idan har 'yan majalisu 159 cikin 316  suka kada kuri'ar amincewa da tsigeta.