The Hague: ICC ta wanke Laurent Gbagbo | BATUTUWA | DW | 15.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

The Hague: ICC ta wanke Laurent Gbagbo

Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ta ICC ta wanke tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo da Charles Ble Goude daga dukkan zargi.

Kombibild - Charles Blé Goudé und Laurent Gbagbo

Charles Blé Goudé da tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo da ICC ta sallama

Babban alkalin kotun Cuno Tarfusser ya bayyana wannan hukunci a yayin zaman da kotun ta yi, inda ya ce an sallami Gbagbo da Charles Ble Goude daga da ke zaman na hannun damansa ne saboda rashin isasshiyar shaida, shekaru bakwai bayan da aka cafke shi. Shi dai Gbagbo ana zarginsa ne da cin zarafin dan Adam boyi bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a Cote d'Ivoire  a shekara ta 2010, inda abokin hamaryasa Alassane Dramane Ouattara ya lashe zaben. Rikicin bayan zaben shugaban kasar na shekara ta 2010 dai, ya janyo mutuwar mutane 3,000 ya yin da wasu kimanin dubu 500 suka kauracewa matsugunansu. Tun dai a shekara ta 2016 Gbagbo ke kokarin gamsar da kotun cewa zarge-zargen da ake masa na da nasaba da siyasa.

Elfenbeinküste, Simone Gbagbo (Getty Images/S.Kambou)

Simone Gbagbo mai dakin tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo da masu taya ta murna lokacin da kotu ta sallame ta daga daurin shekaru 20.

Jim kadan bayan sanar da hukuncin kotun, magoya bayansa suka fantsama zuwa gidan iyalansa da ke Cocody, birnin da ke makwabtaka da Abidjan fadar gwamnatin kasar ta Cote d'Ivoire. da take tofa albarkaacin bakinta kan hukuncin kotun, mai dakinsa Simone Gbagbo cewa ta yi: "Na yi amanna matuka da sakin mai gidana, tun da tsare shi ba wani abu a ciki sai siyasa. A yau gaskiya ta bayyana ga kowa da kowa. Na yi kukan murna saboda na ima ina jiran wannan lokacin."

'Yan adawa da dama dai da ke fatan ganin sun karbe mulki daga hannun shugaba mai ci Alassane Ouattara a zaben shekara mai zuwa ta 2020, sun yi maraba da sakin da aka yi wa Gbagbo. Sai dai a cewar Marie-Evelyne Petrus Barry daraktar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International a yankin yammaci da kuma tsakiyar Afirka, sakin Gbagbo da Ble Goude wani abin kaico ne ga wadanda rikicin bayan zaben shugaban kasa na 2010 a Cote d'Ivoire ya shafa. 

 

Sauti da bidiyo akan labarin