Thailand: 'Yar shekara 37 ta kasance Firaminista
August 18, 2024Shinawatra 'yar shakara 37 ta kasance Firaiminista mafi karancin shekaru da ta hau kan karagar mulkin kasar tun bayan da kotun kundin tsarin mulkin kasar ta sallami tsohon Firimiyan kasar Srettha Thavisin.
Karin bayani: Kotu ta dakatar da firaministan Thailand
Paetongtarn da ke kasancewa 'ya ga tsohon Firaiministan Thailand Thaksin Shinawatra, ta samu kaso biyu bisa uku na yawan kuri'un da 'yan majalisar dokokin suka kada. Kazalika ita ce mace ta biyu da ta kasance Firaiministar kasar kuma ta uku a zuri'ar Shinawatra, da suka mulki kasar.
Karin bayani: Matsalolin kafa gwamnatin Thailand
Mahaifinta Thaksin Shinawatra, ya fuskanci kalubale da dama akan karagar mulki musamman dambarwar siyasar kasar wanda hakan ya sanya shi gudun hijra na tsawon shekara 15, wanda ya dawo gida a 2023.