Thailand: ′Yar sarki ta janye daga tsayawa takara | Labarai | DW | 11.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Thailand: 'Yar sarki ta janye daga tsayawa takara

Hukumar zabe a Kasar Thailand ta amince da janye takarar kaunar sarkin kasar daga neman matsayin firaminista.

Gimbiya Ubolratana ta bayyana takarar ce bazata a ranar Juama'a da ta wuce a karkashin tutar wata jam'iyyar ta kusa ga Tahksin Shinawatra tsohon firaministan kasar abokan gabar gidan saurartar na Thailand kafin daga bisani ta janye. Hukumar zaben Thailand ta ce 'yan sarki ba su da yancin shiga harkokin siyasa. Nan gaba ne a ranar 24  ga watan Maris za a yi zaben 'yan majalisun dokokin a Thailand.