1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama ta biyo bayan haɗewar Rasha da Kirimiya

March 18, 2014

Vladimir Putin na Rasha ya nuna bai ji daɗin kutsen da ƙasashen yamma suke yi a tsakaninsa da yankin Kirimiya ba, kuma ya ce Rasha za ta rama

https://p.dw.com/p/1BRWl
Krim Vertragsunterzeichnung 18.03.2014
Hoto: Reuters

Fadar Kremlin ta ce yanzu yankin Kirimiya ya haɗe da Rasha a hukumance, wannan ya zo ne bayan da ɓangarorin suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta tabbatar da hakan, duk da adawar da wannan mataki ke fiskanta daga al'ummar ƙasa da ƙasa, waɗanda suka haƙiƙance cewa mashigin tekun Bahr Aswad mallakin Ukraine ne.

Fadar ta Kremlin ta fitar da wannan labarin ne 'yan mintoci ƙalilan da sanya hannun shugaba Vladimir Putin da shugabanin yankin na Kirimiya, kan wannan yarjejeniya.

Gabanin sanya hannun dai, a wani dogon jawabin da ya yi wa majalisar dokokin ƙasar ta Duma inda aka riƙa tafi ana nuna masa goyon baya, Putin ya yi iƙirarin cewa Kirimiya da Rasha suna da dangantaka ta ƙut da ƙut ya kuma yi Allah wadai da shawarar da aka ɗauka lokacin daular Sobiet, inda Nikita Khrushchev ɗaya daga cikin waɗanda suka jagoranci daular lokacin yaƙin cacar baka, ya miƙa yankin na Kirimiya ga Ukraine, yana mai cewa abu ne da ya saɓawa dokoki da dama, kuma ƙuri'ar raba gardamar ran asabar ta kafa tarihi mai mahimmanci.

Shugaba Vladamir Putin bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen cewa ƙasarsa za ta ɗauki yunƙurin ƙasashen yamma na firgita ta da takunkumi dan kada ta haɗe da kirimiya, a matsayin wani cin zarafi kuma Moskow za ta rama.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman