1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da sabon wa'adin mulki sun mutu

Abdoulaye Mamane Amadou
November 17, 2019

Hukumomi a kasar Guniea sun tabbatar da mutuwar mutane tara sakamakon zanga-zangar kin jinin tazarcen da shugaba Alpha Condé ke son aiwatarwa ta hanyar gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/3RQDS
Guinea Conakry | Proteste & Ausschreitungen
Hoto: Getty Images/AFP/C. Binani

Hukumomi sun ce wadanda suka mutun galibinsu mazauna birnin Conakry ne, kuma sun halaka ne sakamakon boren da ya yi sanadiyyar jikkata wasu da dama baya ga barnata dukiyoyi da kadarorin gwamnati.

Rahotanni sun bayyana cewa ko a ranar Larabar da tagabata ma, an samu barkewar rikici tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro a unguwanni da dama a Conakry babban birnin kasar.

Tuni dai manyan jami'an diflomasiyya ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da ECOWAS da Kungiyar EU, suka yi kira ga bangarorin kasar da su hau kan teburin tattaunawa domin warware rikicin, a yayin da Amirka da Faransa suka ce sakin wadanda aka kama sakamakon zanga-zangar, ka iya taimakawa wajen kashe wutar rikicin.