Tayin tantance ′yan gudun hijira kafin su shiga Jamus | Labarai | DW | 12.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tayin tantance 'yan gudun hijira kafin su shiga Jamus

'Yan siyasar Jamus na bukatar a samar da wani wuri kan iyaka wa 'yan gudun hijira su ya da zango dan a tantance su.

Bisa la'akari da tudadowar da 'yan gudun hijira suke yi a Jamus, 'yan siyasa a jam'iyya mai ci ta CDU da 'yar uwarta CSU sun ce ya kamata a kebe wani wuri a bakin iyakar Jamus dab da inda 'yan gudun hijirar suke shigowa, a mayar da shi inda za su rika yada Zango har sai an tantance ko suna da damar samun 'yancin zama a kasar kafin a bar su su shigo. Sabon mai kula da 'yan gudun hijiran ya ce 'yan siyasar za su tattauna yiwuwar wannan batu daga nan zuwa mako mai zuwa, sai dai Jam'iyyar adawa ta SPD, wadda ita ma ke hadakar gwamnatin kasar na tababan yiwuwar aiwatar da wannan tsari.

Kwamishanan kula da masu gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin Turan da su dauki 'yan gudun hijirar daga sansanoni da ma kasashen da ke wajen kasashensu na asali, domin a cewarsa wannan ne hanyar mutunta dan adam ta yadda ba sai sun kashe magudan kuaden da wata sa'a ba su da shi ba, ko kuma sun sanya rayukansu a cikin hadari.