1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afuwa ga masu dauke da makamai

Gazali Abdou Tasawa/YBNovember 4, 2015

A Burundi a dai dai lokacin da ake rade-radin bayyana wata kungiyar tawaye a kasar shugaba Pierre Nkurunziza ya yi tayin yin afuwa ga duk wadanda za su amince su mika makamansu nan zuwa karshen mako.

https://p.dw.com/p/1Gza1
Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaba Pierre NkurunzizaHoto: picture-alliance/dpa/C. Karaba

Shugaban ya yi wannan tayi ne a cikin wani jawabi da ya gabatar a gidajen radiyo da na Talabijin na kasar. Jawabin da shi da kansa ya haifar da mahawara da ma kara haifar da fargaba a zukatan al'ummar kasar.

Shugaba Pierre Nkurunziza ya yi wannan tayi na yin afuwa ga mutanen da za su mika makaman nasu nan zuwa karshen wannan mako a cikin jawabin nasa wanda ya gabatar a cikin harshen Kirundi na kasar. Sai dai manazarta da dama a kasar ta Burundi na ganin jawabin shugaban kasar jawabi ne da ke cike da barazana a maimakon neman sulhun. Pascal Niyonizigiye mai sharhi kan al'amuran siyasar duniya kuma malami a jami'ar Bujumbura na daga cikin masu irin wannan ra'ayi.

"Lalle karbe makamai ba laifi ba ne abin alkhairi ne ma ga tsaron lafiyar al'umma. Sai dai matsalar a nan ita ce gwamnati na son yi wa matsalar kasar fassara da rikicin kabilanci alhali kowa ya san matsala ce da ke da nasaba da batun gudanar da milki. Kuma mulkin na fuskantar matsala ta rashin kudi na gudanarwa. Hakan ta sanya gwamnatin ta kidime ta shiga yin maganganu irin na mulkin danniya wanda kuma mu muke ganin wasu alamu ne na mulkin ya kawo karshe."

Flüchtlingscamp Nyarugusu Tansania
'Yan Burundi da ke zaman gudun hijira a TanzaniyaHoto: DW/P. Kwigize

Ko baya ga shugaba Nkurunziza shi ma shugaban majalissar dattawan kasar ta Burundi Reverien Ndikuriyo ya gudanar da wani taro da masu shugabannin unguwannin birnin na Bujumbura kan wannan batu inda ya yi jawabi a garesu a cikin harshen Kirundi na kasar. Jawabin da Paskcal Niyonizigiye ya ce shi kansa ba na zaman lafiya ba ne.

"Kalmar da suka yi amfani da ita na nufin a yi amfani da adda domin kawar da abokin gaba. A takaice jawabi ne na neman tsorata abokin hamayyar siyasa ta hanyar nuna masa cewa a shirye ake a yi amfani da ko wace hanya domin kawar da shi da rayuwarsa da nufin haifar da fargaba a tsakanin 'yan adawa da ma 'yan farar hula."

wannan tayin sulhu na shugaba Nkurunziza ya zo ne a dai dai lokacin da harakokin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa musamman a babban birnin kasar na Bujumbura.

Beerdigung von Oppositionsmitglied Emmanuel Ndayishimiye in Burundi
Zama cikin fargaba a BurundiHoto: picture-alliance/dpa/AA/R. Ndabashinze

Yanzu dai kwanaki biyu suka rage wa'adin da shugaba Nkurunziza ya bai wa masu rike da makaman da su yi saranda tare da mika makaman nasu, kuma duniya ta zura ido ta ga amsar da masu dauke da makaman za su bayar.