Tayar da ƙayar bayan sojoji a Guinee Bisau | Labarai | DW | 01.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tayar da ƙayar bayan sojoji a Guinee Bisau

Kuratan sojojin Guinee Bisau sun kama firaministan ƙasarsu wato Carlos Gomes Junior.

default

Kuratan sojoji

Rahotanni da ke zuwa mana da ɗumi-ɗuminsu daga birnin Bisau sun nunar da cewa wasu kuratan sojojin Guinee sun kama firaministan ƙasar, wato Carlos Gomes Junior. Jami´an tsaron ƙasar sun nunar da cewa babbar tashar rediyo mallakar gwamantin ta katse shirye-shiryenta, tare da sanya baitocin yabon sojoji. Babu wata sahihiyar kafa da ta baiyana ko yunƙurin juyin mulki me koko´a´a. Sai dai tsafke firimiyan na Guinee Bisau ya zo ne sa´o´i ƙalilan bayan dirar miƙewa da dakarun suka yi a cibiyar Majalisar Ɗinkin Duniya domin ceto komadan sojojin ruwa wato Bubo Nat Tchoto da aka tsare bisa zargin yunƙurin kifar da gwamanti. A tattaunawa da yayi da kanfanin dillacin labaran Reuters, jakadan wata ƙasa ta Turai da ke birnin Bisau ya ce rikicin bai kai fadar shugaba Malam Bacai Sanha ba tukuna.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu