Tattaunawar zaman lafiya a Geneva | Labarai | DW | 31.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawar zaman lafiya a Geneva

'Yan tawayen Siriya da yanzu su ke Geneva sun ce sun fara wani zama da manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin na Siriya Staffan de Mistura gabannin hawa kan teburin sulhu.

Mai magana da yawun 'yan tawayen ya ce zaman sharar fage ne na tattaunawa da ake son su halarta kuma gabannin taron za su tabbatar da cewar an biya musu bukatunsu musamman ma batun killace wuraren da suke rike da su wanda gwamnatin Bashar al-Assad ta yi.

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Siriya din ya ce tattaunawa da 'yan tawayen suka amince su yi da shi alama ce ta kai wa ga samun daidaito a yunkurin da suke yi na wanzar da zaman lafiya.