Tattaunawar tsaro tsakanin NATO da Rasha | Labarai | DW | 20.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawar tsaro tsakanin NATO da Rasha

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO za ta gudanar da wani muhinmin taro da Rasha, wanda ke zuwa a karon farko tun bayan da yankin Kiremiya na Ukraine ya hade da Moscow a 2014

Tattaunawar wani mataki ne na sassauta rikicin yankin Tekun Balkan da rikicin yaki da ke cigaba a yankin gabashin Ukraine. NATO ta yanke dangantaka da Moscow domin nuna rashin jin dadinta da wannan yunkuri.

Dangantakar ta kara muni sakamakon yakin da Moscow take yi a Siriya, daura da tayar da jijiyar wuya cikin makon daya gabata sakamakon arangama tsakanin sojin Amurka da jiragen Rasha a Tekun Balkan.

Anasaran jakadun kasashe 28 da ke da wakilci a kungiyar kawancen ta NATO ne za su hadu da jami'an kasar ta Rasha a birnin Brussels a wannan Larabar, domin tattauna rikicin Ukraine da inganata dangantakar soji kana da yakin kasar Afganistan.