1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soja sun fara tattauna wa da bangarorin siyasar Guinea

Abdoulaye Mamane Amadou
September 14, 2021

Sojojin da suka kifar da gwamnati a Guinea Conakry, sun fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki na al'ummar kasar a wannan Talata, a wani yunkuri na mika jan ragamar mulkin kasar a hannun farar hula.

https://p.dw.com/p/40JMc
Guinea | Mamady Doumbouya
Hoto: CELLOU BINANI/AFP/ Getty Images

Za a shafe tsawon kwanaki uku ne a na tattaunawar da bangarori da dabam-daban na al'ummar kasar, ciki har da 'yan siyasa da malamai da sarakunan gargajiya da kungiyoyin fararen hulla da kamfanonin hakar ma'adanu.

Tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Alpha Conde, sojoji suka bayyana aniiyarsu ta sake mika mulki a hannun wata gwamnatin farar hula bayan da suka rusa majalisar ministoci da kundin tsarin mulki. Sai dai kawo yanzu ba su dibarwa kansu wani wa'adi ba.

Ko a yayin wata ziyarar da ya kai a yammacin jiya, wakilin MDD a yankin yammacin Afirka Mahamat Saleh Annadif, ya ce yana fatan wa'adin zai kasance madaidaici wanda kuma 'yan kasar ta Guinea da kansu za su zaba.